Ma’aikatan Kananan Hukumomin Adamawa Sun Shiga Yajin Aikin Sai “Baba Ta Gani”

Ma'aikatan kananan hukumomin jihar Adamawa a karkashin kungiyarsu NULGE, ke nan suka mamaye harabar majalisar dokokin jihar

Yanzu haka rahotanni daga jihar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya, na cewa abubuwa sun tsaya cik a dukkan kananan hukumomi 21 na jihar sakamakon yajin aikin da ma’aikatan kananan hukumomin suka soma .

Ma’aikatan sun shiga yajin aikin ne sakamakon rashin samun albashinsu na watanni biyar.

Wasu fusatattun ma’aikatan kananan hukumomi a jihar Adamawa sun daura damarar soma yajin aikin sai baba-ta-gani da suka fara daga jiya Talata har illa ma sha Allah.

ADAMAWA: Ma'aikatan kananan hukumomin jihar sun fara yajin aiki

Wannan yajin aikin dai ya tsaida harkokin mulki a daukacin kananan hukumomin jihar 2, inda ma’aikatan suka garkame sakatariyoyin kananan hukumomin jihar.

Da yake ganawa da manema labarai, Commrade Hamman Jumba Gatugel dake zama shugaban Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi Ta Kasa da ake kira NULGE, reshen jihar Adamawa, yace abun takaici ne gwamnatin jihar ke sauke fushinta akan ma’aikatan kananan hukumomi, ta hanyar nuna musu shakulatin bangaro,alhalikuwa ana biyan wasu nau’in ma’aikata.

Gatugel yace ya zuwa yanzu ma’aikatan kananan hukumomi a jihar na bin bashin albashin watanni biyar, wanda domin haka ne suka tsunduma cikin wannan yajin aiki .

To sai dai kuma a nata martini, gwamnatin jihar Adamawan tace ma’aikatan kananan hukumomin basu yi mata adalci ba da suka shiga wannan yajin aiki. Commrade Ahmad Sajo ,kwamishinan yada labaran jihar, yace bashin da ma’aikatan ke bi, bai kaina wata biyar ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Ma’aikatan Kananan Hukumomin Adamawa Sun Shiga Yajin Aikin Sai “Baba Ta Gani” - 3' 44"