A jiya laraba ne ma’aikatan jinya da ungozoma na Nigeria suka fara barazanar soma yajin aiki a duk fadin kasar, abinda ke zuwa a kasa da mako guda da janye yajin aikin da likitocin dake neman kwarewa suka yi.
Ma’aikatan dai, wadanda suka hada da ungozoma da nas nas da kuma na ma’aikatan da ba likitoci ba, suna kuka ne akan rike musu hakkokinsu. Sai dai kuma wannan yajin aiki tuni ya soma tada hankalin jama’a musamman masu karamin karfi da su suka fi zuwa asibitocin gwamnati, kamar yadda wasu a Jalingo da Yola,a arewa maso gabashin Najeriya ke kokawa.
To wai ko me ya ingiza ma’aiktan jinyar takulo batun yajin aiki a yanzu? Mr Yaduma Caleb Filibus wanda shine mataimakin shugaban hadakar kungiyoyin ma’aiktan jinya a babbar asibitin gwamnatin tarayya dake Adamawa, wato FMC-Yola, yace zasu je yajin aikin ne sakamakon shakulatin bangaron da yake zargin cewa gwamnatin kasar na yi game da yarjejeniyar da suka yi tun shekarar 2013.
Ya shaidawa wakilinmu Ibrahim Abdulazeez cewa sun damu kwarai game da wannan matakin da zasu dauka amma basu da zabi ne.
Ga Ibrahim AbdulAzeez da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5