Ma'aikatan Filato Sun Janye Yajin Aikin da Suka Shiga

Wasu ma'aikata

Kungiyar kwadago reshen Filato ta sanarda janye yajin aikin da ma'aikatan jihar suka shiga

Kungiyar kwadago reshen Filato ta janye yajin aikin da ma'aikata suka shiga.

Ma'aikatan sun yi makonni hudu nuna yajin aikin bayan gwamnatin Jang da ta shude ta gaza biyansu albashinsu na watanni shida. Ma'aikatan sun hada da na jiha da na kananan hukumomi.

A cewar shugaban kungiyar kwadago ta jihar Filato Jubril Banchir yace kungiyar ta janye yajin aikin ne biyo bayan yarjejeniyar da suka cimma da sabuwar gwamnatin jihar ta Simon Lalong. Gwamnatin ta yadda ta biya albashin watanni biyu cikin wannan makon. Yace gwamnatin ta rokesu da su janye yajin tare da yin alkawarin biyan albashin watanni biyu kafin gwamnati ta samu kudi daga gwwamnatin tarayya.

Bayan kwana bakwai zasu koma kan teburin shawara domin sasanta alamuran dake tsakaninsu da gwamnati. Suna harsashen za'a warware matsalolin cikin kwanaki talatin. Idan kuma basu gama ba basu ki karin lokaci ba.

Ma'aikatan suna fata gwamnati zata cika alkawarin da tayi. Idan kuma ta yaudaresu zasu koma yajin aikin. Ma'aikatan suna sane da cewa sabon gwamnan ya nemi bashi ne ya biyasu domin ya gaji bashin nera biliyan 104.

Ga rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan Filato Sun Janye Yakin Aikin da Suka Shiga - 3' 39"