A duk fadin duniya, ba kasafai ne gwamnati ke barin ma'aikatanta su shiga wata harka ba, musamman wacce za ta iya karo ko kawo cikas ga aikin da mutum ke gudanarwa.
WASHINGTON D.C. —
A Jamhuriyar Nijar wani ma’aikacin gwamnati a sashen shari'a wanda a sakamakon sha’awar sana’ar kida da waka irin na zamani ya kafa kungiya da ake kira "Tal National."
Kuma a ‘yan shekarun nan kungiyar tana tashe musamman a wurin mata, abinda ya sa suke gayyatar wannan kungiya domin cashewa a bukukuwa daban daban.
Isufu Almeida, wani akawun kotu ne kuma ya ke jagorantar wannan kungiyar ta Tal National.
Yayin da wasu su ke ganin babu laifi idan ma'aikacin kotu ya shiga wata harka kamar ta kida, wasu na ganin lamarin zai iya yin karo da aikinsa na banagren shari'a.
Wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma ya yi hira da shi a wannan rahoto da za ku ji:
Your browser doesn’t support HTML5