Ma'aikatan Gwamnatin Jihar Neja Sun Ki Komawa Bakin Aiki

Yan Kwadago

Ma'aikatan gwamnatin jihar Neja a Najeriya sunki komawa bakin aiki bayan da kungiyar kwadagon Najeriya ta janye yajin aikin gama gari a ranar litinin din da ta gabata. Ma'aikatan sunce sunki komawa bakin aiki ne saboda dama can akwai tsimammiya a tsakanin su da gwamnatin jihar Nejan.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar Yahaya Idris Nyako yace an cire musu kudin hutu kuma an ki a dawo dashi, dan haka suka ce basu dawowa sai gwamnati ta biya musu bukatar su.

Saidai gwamnati ta nuna bacin ranta, inda ta ce kungiyar kwadagon bata bi tsarin daya kamata ba kafin ta yanke hukuncin tafiya yajin aiki. Kuma bayan wata 'yar takaddama, kungiyar kwadagon jihar ta umarci ma'aikatan gwamnati da su koma aiki a jiya Laraba.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari domin karin bayani...

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan Gwamnatin Jihar Neja Sun Ki Komawa Bakin Aiki- 2'57"