Shugaban Ma’aikatar na farar hula, Didam Joel, ya ce an tsare wani ma'aikacin farar hula na ma'aikatar har tsawon wata guda a hannun hukumomin soji, duk da cewa shi ba soja ba ne.
Joel ya kara da cewa an kuma ci zarafin wani ma'aikaci mai rike da mukamin mataimakin darakta a ma’aikatar da ke aiki a Makarantar Sakandare ta Command, Ojo, a Legas, a jiya ba tare da bin ka’idojin aikin gwamnati ba.
Duk da dai cewa ya zuwa yanzu rundunar sojin kasar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da wannan zargi ba, daya daga cikin Kungiyar Manyan Ma’aikatan Kasar ta Najeriya (ACSSN) a rundunar sojin Najeriya, Abuja, ya bayyanawa manema labarai sunan Ambrose Akhigbe a matsayin wanda aka ci zarafinsa a ranar Litinin da ta gabata .
Ya kuma kara da zargin cewa an kashe wani masanin kimiyar dakin gwaje-gwaje a Asibitin Naval Reference, a Garin Navy, da ke Ojo, a Legas, ‘yan watanni biyu da suka gabata.