Wasu ma'aikata a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, sun yi zanga zangar lumana, game da rashin biyansu albashinsu na kusan watanni shida.
Su dai ma'aikatan maza da mata, na daga cikin ma'aikatan da tsohuwar gwamnatin APC ta Sanata Muhammadu Bindo Jibrilla ta dauka aiki, a shekarar 2018.
Tun shigowarta, gwamnatin PDP ta Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, ta dakatar da wa'adannan ma'aikata bisa dalilan cewa sai ta gudanar da bincike.
Gwamnatin ta kafa kwamitocin binciken ma'aikatan, wanda kawo yanzu ba a fayyace ma su makomarsu ba.
Da yake tarbar ma'aikatan, wadanda ga dukkan alamu suke cikin fushi, kamar yadda wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya lura, mataimakin gwamnan jihar Adamawan Chief Crowther Seth, ya bukace su da su kwantar da hankulansu inda ya ce gwamnati za ta sake duba lamarinsu da idon rahama.
Kawo yanzu kungiyar kwadago ta NLC a jihar ba ta ce komi ba yayin da wasu ma'aikatan ke cikin halin ni 'yasu sanadiyyar rashin biyansu albashin.
Matsalar rashin biyan ma'aikata albashi, ba bakon abu ba ne a Najeriya, inda a duk lokacin da wata sabuwar gwamnati ta hau karagar mulki, ta kan dakatar da biyan ma'aikata domin ware na bogi.
Hukumomi kan ba da hujjar cewa, hakan mataki ne na rage yawan kudaden da jiha kan kashe, yayin da wasu ke zargin cewa dabara ce ta muzgunawa gwamnatin da ta shude, musamman idan ta adawa ce.
Amma kamar yadda masu lura da al'amura ke nunawa, a wasu lokuta daukan irin wannan mataki kan jefa ma'aikatan da ba su ji ba ba su gani ba cikin halin kakanikayi.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:
Your browser doesn’t support HTML5