Rahotanni a Najeriya na nuni da cewa, ana samun karuwar kisan kai, da kwararru ke dangantawa da matsin rayuwa da kuma rashin kwanciyar hankali.
Ganin munin wannan al’amari, a ranar Lahadi wata kungiyar dake fafatukar shawo kan kisan kai da ake kira Africa Porject Against Suicide ko kuma APAS, a takaice ta sanar da shirin gudanar da wani gagarumin taro a birnin tarayya Abuja, na masu ruwa da tsaki da nufin shawo kan wannan matsalar da take ci gaba da janyo asarar rayuwa.
Ko a jiya Talata an sami aukuwar irin wannan lamarin a garin Maiduguri inda wani tsohon kukun gwamnan Kashim Shatimma ya kashe kansa.
Wakilinmu Haruna Dauda Bi’u yaje fadar gwamnatin jihar Borno inda wannan lamarin ya faru ga kuma rahoton da ya hada mana.
Your browser doesn’t support HTML5