Luka Modric Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Na Duniya

Dan wasan tsakiya na kungiyar Real Madrid Luka Modric, dan asalin kasar Croatia ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa wanda Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Fifa da take bayarwa duk shekara a bikin da aka gudanar a birnin London, ranar Litinin.

Modric ya kawo karshen baba-keren da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka yi wajen lashe kyautar a tsakaninsu cikin tsawon shekaru goma. Modric mai shekaru 33 ya doke Cristiano Ronaldo na Juventus da kuma Mohamed Salah na kungiyar Liverpool a bana.

Modric dan kasar Croatia, ya lashe kofin zakarun nahiyar Turai karo na uku a jere a kungiyarsa ta Real Madrid, bayan haka ya jagoranci kasarsa ta Croatia, zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 da aka yi a Rasha inda suka kare a matsayi na biyu.

Ku Duba Wannan Ma Christiano Ronaldo Ya Fita Daga Filin Wasa Yana Kuka

Modric ya samu kashi 29.05℅ Cristiano Ronaldo ya samu kashi 19.08℅ inda ya zamo na biyu sai Mohammed Salah da kashi 11.23℅ a matsayi na uku. Cristiano Ronaldo bai sami halartar bikin karramawar ba, inda wasu ke ganin hakan bai daceba.

Mohamed Salah ya lashe Kyautar Puskas, wadda ake ba dan wasan da ya jefa kwallo mafi kyau a raga. Ko da dai wasu na ci gaba da jinjina wa Ronaldo kan kwallon da ya jefa ragar Juventus a bara a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wadda ta kai ga magoya bayan Juventus a taron mikewa tsaye don girmama shi.

Sai dai kuma Salah baya cikin jerin ‘yan wasan FIFA 11 da suka fi iya taka leda duk da cewa yana cikin 'yan wasa 3 da suka yi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan bana.

Shima tsohon mai tsaron raga na Chelsea, Thibaut Courtois, ya lashe Kyautar mafi kyawun mai tsaron raga a bana, amma kuma baya cikin 'yan wasan Fifa 11 da ta zaba.

‘Yan wasan sune kamar haka:

Maitsaron raga

David de Gea (Manchester United)

Masu tsaron gida

Dani Alves (Paris Saint-Germain)

Raphael Varane (Real Madrid)

Sergio Ramos (Real Madrid)

Marcelo (Real Madrid)

‘Yan wasan tsakiya

Luka Modric (Real Madrid)

N'Golo Kante (Chelsea)

Eden Hazard (Chelsea)

‘Yan wasan gaba

Lionel Messi (Barcelona)

Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain)

Cristiano Ronaldo (Juventus)

Kocin kasar Faransa, Didier Deschamp shi aka zaba a matsayin gwarzon mai horaswa na shekarar 2018 inda ya doke Zinade Zidane, da kuma Zlatko Dalic.

Your browser doesn’t support HTML5

Luka Modric Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasa Na Duniya