Luis Figo Ya Janye Daga Neman Shugabancin FIFA

FIFA Election

Luis Figo ya fitar da kansa daga cikin jerin ‘yan takarar neman shugabancin hukumar kwallon ‘kafa ta FIFA, ya bar wa shugaban hukumar na yanzu Sepp Blatter da tsohon ‘dan kwamitin zartarwar hukumar Sarki Ali bin Al-Hussein domin su fafata.

Figo dai na cikin takaicin yadda Sepp Blatter yaki amincewa kan fitowa ayi muhawara da ‘yan takara suka saba yi, yana kuma ganin shekaru goma sha bakwan da shugaban hukumar ya shafe yana mulki a matsayin shugabancin kama karya ne.

Shi dai tsohon shahararren ‘dan wasan daya buga wasanni a manya manyan kulub a baya kamar su Real Madrid da Bercelona, yayi da’awar cewa “wannan wani abune ba zabe ba”. ya cigaba da cewa wannan wata hanya ce ta zaben kaitsaye wadda zata baiwa mutum ‘daya duk karfin mulki, ni bazan bi wannan hanyar ba.

Figo ya bayyana cewar sakamakon zuwa tarurrukan zakarun nahiyoyi a fadin duniya, da cewar ya ga wasu alamomin da zasu baiwa masu ra’ayin son ganin kwallon kafa ta wanzu cikin tsafta da rashin kumbiya kumbiya.