Magajin Garin London ya amince da bukatar wasu masu zanga-zanga ta su saki wani balam-balan mai siffar Shugaban Amurka Donald Trump a fusace, saye da kamfai tamkar dan bomboi, yayin da Shugaban na Amurka zai kai ziyara a London, babban birnin kasar Burtaniya.
Balam-balam din mai tsawon mita 6 zai bi ta kan ginin Majalisar Dokokin Burtaniya da misalin karfe 9:30 na safe agogon yankin, a ranar 13 ga watan Yuli da za a yi zanga-zangar.
"Magajin Garin na goyon bayan zanga-zangar lumana tare kuma da sanin cewa hakan na iya haifar da wani abu,"
a cewar ofishin Magajin Garin na London Sadiq Khan a jiya Alhamis.
Leo Murray, dan rajin da ya jagoranci kirkiro balam-balam din, wanda ake wa lakabi da "Trump Dan Bomboi," ya yi amfani ne da kafar internet wajen tara kudi dala dubu ashirin wajen gina, abin da ya kira, "balam-balam dinmu mai tsawon mita 6 kuma mai ruwan doruwa mai siffar dan bomboi mai mugunyar fuska da guntayen yatsu, wanda zai bi ta kan tsakiyar birnin London yayin da Trump ke kai ziyara."
A yayin ziyarar ta tsawon kwanaki uku. Trump zai gana da Sarauniya Elizabeth da Firayim Minista Theresa May.