Lokaci Ya Yi Domin Maganin Zaman Kashe Wando - Rukaiya Mohammed

Malama Ruqqaya Abubakar ta ce kasancewar ta kammala karatunta na jami’a hakan bai sa ta dogara da aikin gwamnati ba illa bada kwarin gwiwar kama sana’ar hannu domin dogaro da kai.

Ta ce tana sana’ar kayan tande-tande dangogin fulawa, a duk lokacin da jama’a ke bukata walau na biki ko suna ko wani taro, bayan ta kammala karatu a jama’ar Bayero ta Kano.

Ruqayya ta ce tun da farko ta so ta karanci karatun lauya amma hakar ta bata cimma ruwa ba sai ta sami gurbin karanta harshen Hausa bayan kammala karatun na ne ta fara sana’a.

Ta ce lokaci yayi da mata zasu zamo masu dogaro da kai ta hanyar yin kananan sana’oi don kashe kananan bukatu mussaman na ‘yan uwa da abokan arziki.

Your browser doesn’t support HTML5

Lokaci Ya Yi Domin Maganin Zaman Kashe Wando