Lokaci Ya Yi Da Al'umma Zata Mara Mana Baya - Shehu Madox Tall Black Boy

Mahammad Shehu Madox Tall Black Boy, mawakin hip-hop ya ce kamar kowa sha’awace ta sa ya fara waka kuma ya fara ne tun yana makarantar sakandire da zummar wa’azantarwa da da ilmantar wa.

Daga cikin matsalar da mawaka kan fuskanta sun hada da yadda ake yi masu mummunar fassara hakan ne ma yayi wata waka wacce yayi wa lakabi da Tantiri domin fadakar da alumma cewar shi ba tantiri bane.

Ya ce a nasa salon wakar tana duba ne da yadda al’ummarsa take mussaman ma a fannin nishadantarwa – duba da yadda yanzu aka raja’a ga wakokin wasu harsuna – shima sai ya rera tasa wakar da harshen sa gudun kada ya rasa masu sauraronsa.

Madox ya ce, lokaci yayi da al’umma zata mara masu baya wajen cimma muradunsu- ya kara da cewa sai al’umma ta karbi abinda suke yi ne zasu samu albarka – ya ce shigar da suke yi bata zata abin dogaro da za’a yanke masu hukunci ba akan dabi’unsu da sauransu.

Madox, ya kara da cewa bayan hip-hop yana wakokin party jazz wato wakokin da ake yi a wuraren taro walau na biki ko duk wani taro na farin ciki.

Your browser doesn’t support HTML5

Mahammad Shehu Madox Tall Black Boy