Akalla mutum 16 aka tabbatar sun mutu yayin da wasu da dama suka bata bayan da wani kwale-kwale dauke da daruruwan fasinjoji ya kife a yankin tsakiyar arewacin Najeriya a cewar hukumomi.
Fasinjojin wadanda akasarinsu mata ne da yara kanana, na kan hanyarsu ta zuwa Maulidi ne a lokacin da hatsarin ya faru a daren Talata a cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja, Abdullahi Baba Arah.
Ya kara da cewa kwale-kwalen na dauke ne da mutum 300 yayin da yake tafiya a Kogin Neja a kusa da Mokwa a lokacin da lamarin ya faru da misalin karfe 8:30 na dare.
“Wannan hatsari ya faru ne saboda jirgin nan yana iya daukan mutum 150 zuwa 200, sai ga shi an saka fiye da mutum 300. Shi direban jirgin ya fada musu an wuce mutanen da jirgin yake iya dauka, amma suka tilasta masa sai ya dauke su.” In ji Shugaban Hukumar HYPADEK mai kula da garuruwan da ke gabar tashoshin samar da lantarki a Najeriya, Abubakar Sadik.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an tsinci gawarwakin mutum 16, mata biyu maza 14.