Liverpool Tace Ruwa Ba Sa'an Kwando Bane Ga Barcelona

Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool tayi waje da Barcelona a cikin gasar cin kofin zakarun turai UEFA Champions League, bayan da ta doke ta da jimillar kwallaye 4-3 a wasanni biyu da suka buga a tsakanin su.

A wasan farko da aka buga a Camp Nou, Barcelona ce ta samu nasara daci 3-0, ita kuwa Liverpool a ranar Talata da ta gabata ta bada mamaki a Anfiled inda ta lallasa ta da ci 4-0.

Hakan na nufin ta farke dukkanin kwallaye ukun da Barcelona ta jefa mata a Camp Nou, ta kara daya akai hakan ya bata damar zuwa wasan karshe na gasar a bana, kuma na biyu a jere domin a shekarar da ta gabata 2017/18 Liverpool, ta buga wasan karshe da Real Madrid inda Real ta lashe kofin.

Mai horas da kungiyar ta Liverpool, Jurgen Kloop, ya bayyana nasararsu akan Barcelona, a matsayin wani abin al’ajabi, musamman idan aka yi la’akari cewa, sun buga wasan ne ba tare da manyan 'yan wasansu ba, kamar su Mohamed Salah da kuma Roberto Firmino ba, sabo da rashin lafiya da suke fama dashi.

Kloop, yace ba zai taba mantawa da wannan nasara da yayi akan Barcelona ba, har iya karshen rayuwarsa domin murna ta lullube shi, inda har sai da 'yan wasansa suka zubar da hawaye bayan samun wannan gaggarumar nasarar.

Da wannan nasarar Liverpool ta kai wasan karshe a gasar ta Zakarun Turai a bana, inda take jiran tsakanin Ajax ko kuma Tottenham wadda a yau Laraba 8 ga watan Mayu zasu fafata da juna a karawarsu ta biyu.