Dubban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ne suka tarbi tawagar kungiyar bayan sun sauka a Liverpool daga Madrid.
Liverpool ta samu nasarar lashe kofin gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League na bana kuma karo na shida kenan a tarihinta bayan da ta doke takwararta Tottenham da ci 2-0 a wasan karshea karshen makon da ya gabata a birnin Madrid na kasar Spain.
Shekaru bakwai kenan rabon da Liverpool ta lashe wannan kofin sai dai a shekarar da ta gabata kungiyar ta kai wasan karshe inda Real Madrid ta doke ta.
Ana iya cewa yanzu ta huce fushinta na bara kenan.
Wannan nasara da ta yi ya yi tasiri sosai ga mai horas da kungiyar Jurgen Klopp wanda wannan ne karon farko da ya lashe kofi bayan zuwa wasan karshe sau shida ana doke shi a wasu kulob-kulob da ya jagaoranta kafin zuwansa Liverpool.
Tawagar Liverpool ta yi faretin murnan cin kofin ne cikin wata budaddiyar mota, inda ta bi ta wani layi mai dumbin magoya bayanta da suka yi dafifi don taya su murna.
Liverpool ita ce kungiyar da tafi kowacce kungiya a kasar Ingila yawàn lashe wannan kofi na zakarun turai.