Liverpool, Man City Da Arsenal Na Fafutukar Gasar Zakaru

A cigaba da wasannin da ake bugawa na gasar Firimiya lig a kasar Ingila wadanda suka zamo kwantai saboda wasu dalilai jiya kungiyar Chelsea ta doke Watford da kwallaye 4-3.

Chelsea dai ita ta lashe gasar Firimiya na kasar Ingila a bana yanzu haka tana da maki tasa'in a wasannin 37, da tayi Tottenham tana mataki na biyu da maki tamanin a wasanni 36.

A yau kuma kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata kara da Sunderland a wasan mako na 34, wanda ya zamo kwantai, sai Manchester City, zata karbi bakuncin Westbromwich.

Za'a buga wasan ne da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

A yanzu haka dai kungiyoyi guda uku na kasar Ingila ke fafatukan ganin sun shiga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai mai zuwa na 2017/18 inda ake neman kungiyoyi biyu kacal daga cikin su don shiga gasar.

Kungiyoyi sune Liverpool da take mataki na Uku, a saman teburin da maki 73, a wasanni 37 da tayi, sai Manchester City, da take mataki na hudu da maki 72, a wasanni 36, akwai kungiyar Arsenal da take matsayi na biyar da maki 69 a wasanni 36.

Shi kuwa mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho, yace yanzu ya mayarda da hankalinsa wajan ganin yayi nasarar lashe kofin Nahiyar Turai Europa League 2016/17 domin hakan shi zai bashi damar zuwa gasar UEFA Champions League na 2017/18 mai zuwa.

Manchester United zata buga wasan karshe ne tsakaninta da Ajax ranar laraba 24/5/2017, a yanzu haka dai Manchester United tana mataki na shida a Firimiya lig na bana da maki 65 a wasanni 36 da tayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Liverpool, Man City Da Arsenal Na Fafutukar Gasar Zakaru - 2'43"