Shahararen dan wasan kwallon kafa na kasar ajantina kuma zakaran kwallon kafa na duniya Lionel Messi, yayi amai ya lashe.
Bayan ya bayyana ajiye takalmansa na takawa kasar sa ta Ajintina leda watanni biyu da suka gabata a sakamakon rashin samun nasara da kasar tasa bata yiba a gasar Copa Amerika, inda kasar Chile ta shasu a wasan karshe, sai gashi ya baiyana dawowar sa domin cigaba da taka leda a kasar tasa.
Messi yace ya dawo daga ritayarsa ne saboda soyayya da yake yi wa kasar sa, an baiyana sunan Messi a cikin mutane 27 wanda zasu buga wa arjantina wasa domin samun nasarar zuwa wasannin kofin duniya na 2018, wanda za'a yi a kasar rasha, a cikin jerin sunayen harda da aminsa Mascherano, wanda shima ya furta ajiye takalmansa bayan messi.
A ranar Alhamis da tawuce ne sabon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Ajantina Edgardo yayi zama da ‘yan wasan harna sama da awa guda wanda ake ganin dawowarsu nada nasaba da ganawar da suka yi.v