Lionel Messi Da Cristiano Ronaldo Sune Kan Gaba A La Liga

Lionel Messi na FC Barcelona yana kokarin ketawa da kwallo a tsakanin Ever Banega da Marius Stankevicius na Valencia a karawarsu ta ranar 2 Maris 2011.

Messi dan wasan FC Barcelona shi en ke gaba da kwallaye 27, amma shi ma Ronaldo na Real Madrid yana da 27, sai dai biyar ya ci ne da bugun fenariti

Lionel Messi na kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona da Cristiano Ronaldo an Real Madrid su na da kwallaye 27 kowannensu a raga ya zuwa jiya lahadi, 6 Maris, 2011, amma Messi ne yake kan gaba saboda kwallaye biyu kawai daga ciki ya jefa ta hanyar bugun fenariti.

Shi kuwa Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye biyar en ta hanyar bugun fenariti.

Sauran ;yan wasan Barcelona dake cikin wadanda suka fi jefa kwallaye a bayan shi Messi dan kasar Argentina, sune David Villa mai kwallaye 17 da kuma Pedro Rodriguez mai kwallaye 13.

Ga jerinsu nan a kasa. Lambar da aka sanya cikin wannan alama ( ) ita ce yawan kwallayen da aka jefa ta hanyar bugun fenariti:

Lionel Messi, Barcelona, 27 (2)

Cristiano Ronaldo, Real Madrid, 27 (5)

David Villa, Barcelona, 17

Fernando Llorente, Athletic Bilbao, 15

Giuseppe Rossi, Villarreal, 14 (3)

Pedro Rodriguez, Barcelona, 13

Felipe Caicedo, Levante, 11

Nilmar, Villarreal, 11

David Trezeguet, Hercules, 10 (1)

Luis Fabiano, Sevilla, 10 (2)

Alvaro Negredo, Sevilla, 10 (2)