Lional Messi Da Wasu Sun Lashe Kyautar Bana

Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Ajantina mai taka leda a kulob din Barcelona, Lional Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasa, wanda hukumar kula da kwallon kafa (FIFA) take bayarwa, tun daga shekara ta 2017.

Wannan shine karo na 6 da ake zabar dan wasan Messi a matsayin gwarzon dan kwallon duniya, ya fara lashe wannan a 2009, 2010, 2011, 2012 da kuma 2015 sai a wannan shekara 2019.

Messi ya haura kan takwarorunsa Christiano Ronaldo na kungiyar Juventus, da kuma Virgil Van Dijk na Liverpool. Haka kuma kocin Liverpool Jurgen Klopp ne ya lashe kyautar mai horaswa mafi hazaka a bana.

Klopp ya doke abokan hamayya da suka hada da kocin Manchester City
Pep Guardiola da kuma Mauricio Pochettino.

A bangaren Mata kuwa 'yar wasan tawagar kasar Amurka Megan Rapinoe ita ce ta lashe kyautar gwarzuwar shekara.

A bangaren masu horarwa a kwallon mata kuma, Jill Ellis ce ta lashe kyautar mai horaswa a bangaren Mata bayan da ta jagoranci tawagar kasar Amurka, suka lashe Kofin Duniya na 2019 a kasar Faransa.

A sashen 'yan wasa Alisson Becker mai tsaron ragar Liverpool shi ne
golan da yafi hazaka shi a aka bai wa kyautar.

Bayan haka kuma an zabi kwallo mafi kyau da aka sha (Puskas) wanda Dan shekara 18 Daniel Zsori, ya lashe kyautar kwallon da ya jefa a minti na 93 a wasan da kungiyarsa ta Debrecen ta yi da Ferencvaros a gasar lig na kasar Hungry, An gudar da bukin ne a birnin Millan.