Bayan sallar idi,limamin babban masallacin kasa dake Abuja Farfesa Shehu Sa'id Galadanci, ya kira 'yan siyasa da su yi takatsantsan saboda babban zabe da za'a gudanar shekara mai zuwa.
Farfesa Galadanci ya roki 'yan siyasa da su yi kokarin ilmantar da magoya bayansu tare da wayar da musu da kai kan neman zaman lafiya ta hanyar kaucewa hatsaniya.
Shi ma ministan babban birnin tarayya Muhammad Musa Bello, ya bayyana ranar sallah a matsayin babbar rana dake da matukar mahimmancin gaske. Ya nemi shugabanni a duk matakai su ji tsoron Allah.
Wadansi mazauna birnin na Abuja suna da ra'ayi mabanbanta gameda irin hali da sallar ta same su a ciki. Yayinda Haji Hafsat Sha'aibu ke yiwa Allah godiya saboda koshin lafiya da mallakar abun yin abun sallar, wani cewa ya yi mutane da yawa na cikin wani irin halin rayuwa, saboda shi kansa layyar hadaka ya yi domin rashin kudi.
Akwai wanda ya yiwa Allah godiya kasancewa ya na da rai amma bai samu ya yi yanka ba sanadiyar fama da rashin kudi.
Yanzu dai mata da yara suna kai da kawowa a wuraren shakatawa a ci gaba da bukukuwan sallar.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Your browser doesn’t support HTML5