Likitocin Tiyatar Zuciya Sun Dauki Matakin Ceton Masu Fama Da Cutar a Najeriya

Wani mai fama da cutar zuciya

Likitocin da ke tiyatar zuciya a Najeriya sun fara daukar matakin shawo kan karamcin cibiyoyin tiyatar zuciyaa kasar.

Likitocin sun dauki wannan matakin ne da nufin shawo kan babbar barazanar da suka ce karancin cibiyoyin jinyar na yi a yunkurin ceto rayukan masu fama da cututukan a daidai lokacin da adadin masu kamuwa da ita ke kara hauhawa.

Wannan yasa suka kara azama domin ganin an samu karin cibiyoyin musamman a yankin arewacin kasar inda yanzu haka babu tsayayyar cibiya da ake tiyatar zuciya akai-akai.

Bayanai daga likitocin tiyatar zuciya ‘yan Najeriya sun nuna cewa, a tsawon shekara daya ana samun wadanda suka kamu da cutar zuciya kimanin dubu 50 zuwa 80, kuma wadanda ake iya yiwa aiki a kasar adadinsu ba zai wuce 200 ba.

Wani yaro da aka yi wa tiyatar zuciya

Hakan kan iya tilasta masu zarafi fita kasashen waje domin neman waraka, yayinda marasa hali kuwa sai dai su zura ido ganin abinda hali yayi, kamar yadda wani magidanci Haruna Sulaiman Idris wanda yaron sa ya kamu da ciwon zuciya ya shaidawa Muryar Amurka.

likitoci-sun-tsunduma-yajin-aiki-a-najeriya

ana-samun-nasara-a-yaki-da-kanjamau-naca

codvid19-najeriya-za-ta-kashe-n400b-kan-rigakafi

Tiyatar zuciya dai acewar shugaban sashen kula da fidar zuciya a asibitin koyarwa ta jama'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato Dr. Abubakar Umar aiki ne mai hadarin gaske.Bisa ga cewarshi, ba a Najeriya kadai ba, ko a kasashen waje ana bukatar likita da ke da kwarewar gaske, kuma wannan ba aiki ne na mutum guda ba. Tilas a sami tagawar ma'aikata da kowa ya san aikin da ya kamata ya yi, ya kuma san aikin sosai.

Masu fama da cutar zuciya

Duba da yanayin da ake ciki a Najeriya dangane cututukan zuciya yasa likitocin zuciya ‘yan kasa suka dauki matakin yin gangamin fadada ayyukan tiyatar inda suka hadu a asibitin koyarwa ta jama'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato a arewacin Najeriya inda i zuwa lokacin rubuta wannan rahoton suka riga su ka yiwa marasa lafiya biyu tiyata cikin nasara da rahusa.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dr. Uvie Onakpoya, shugaban kungiyar likitocin masu tiyatar zuciya a Najeriya ya bayyana cewa,

“ Aikin tiyata mai sarkakiya a zuciya aiki ne da ake iya yi a Najeriya abinda ya tabbatar da hakan shi ne lokacin da aka shiga kulle saboda cutar korona likitocin kasashen waje basu shigowa Najeriya saboda kullen wadannan asibitoci ‘yan kalilan dale akwai a Najeriya sun ci gaba da yin aikin tiyatar zuciya, akan haka ne ma muka yanke shawarar cewa a wannan shekara zamu kokarta muga yadda za a iya fadada cibiyoyi da ke iya wannan aikin. A arewa kacokam babu asibitin da ke wannan aikin akai-akai, amma dai yanzu muna fatar asibitin UDUTH ta Sakkwato zai zamo na daya da zai fara gudanar da wannan aikin a arewa.“

Wannan matakin kan iya taimakawa wajen ceto rayukan masu fama da matsalolin zuciya musamman marasa karfi wadanda akasari suka dogara ga samun shigowar likitocin kasashen waje dake ayyukan jinkai kamar yadda likitocin kasar Morocco suka bayar da agaji a shekarar 2019 da na kungiyar musulmi ta duniya a 2021.

Da irin wannan gangamin da likitocin ke yi na zagayawa suna gudanar ayukkan tiyatar zuciya, sun ce muddin za'a samu goyon baya yadda ya kamata daga hukuma da kuma shawo kan kalubalen da kan kawo tarnaki ga ayukkan, za a samu nasarar ceto rayukan masu fama cutar da kuma hana ‘yan kasa kashe makudan kudi wajen tsallakawa kasashen ketare don neman waraka daga cutukan.

Saurari cikakken rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Likitocin Tiyatar Zuciya Sun Dauki Matakin Ceton Rayuka-3:00"