A cewar sakatare janar na kungiyar likitocin Kenya, Thuranira Kaugiria sun fara yajin aikin ne karfe 12 na dare a yau Juma'a.
Ya ce likitoci 320 wadanda gwamnatin birnin Nairobi ta dauka aiki ne suka fara yajin aikin saboda dumbin matsalolin da suke fama da wadanda suka hada da rashin kayayyakin kariya da kuma rashin wuraren kebe masu cutar COVID-19.
Yajin aikin ba zai shafi asibitoci masu zaman kansu da kuma wadanda ke karkashin gwamnatin tarayya ta kasar ba.
Dama dai likitoci a Kenya sun yi ta wallafa hotuna a shafukansu na Twitter domin nuna irin kayayyakin da ake ba su domin kare kai wadanda suka kira marasa inganci.
Alkaluman baya-bayan nan dai sun nuna cewa akalla mutum 31,441 ne ke dauke da cutar a kasar yayin da mutum 532 suka mutu sakamakon cutar.