Likitoci Zasu Fara Aika Magani Ga Marasa Lafiya Ta Sararin Sama

Hukumomin kamfanin gidan waya mafi girma na kasa-da-kasa a duniya UPS, ya kammala shiri tsaf don fara isar da sakonnin magunguna na likitoci a gidaje ga marasa lafiya.

Tsarin dai zai baiwa likita damar aika magani daga gidan magani zuwa gidan duk wani marar lafiya, ta hanyar amfani da na’urar mai sarrafa kanta da ake kira "Drone".

Za’a fara gwajin sabon tsarin ne a wasu jihohin Amurka guda biyu nan da makonni kadan masu zuwa, wannan shine karon farko da za’a aiwatar da wannan shirin, wanda a baya na’urar drone na isar da sako zuwa makarantu da asibitai, amma yanzu likafa ta ci gaba.

Shugaban jigila da tsare-tsaren kamfanin UPS Mr. Scott Price, ne ya sanar da hakan a ofishin su dake jihar Atlanta, wanda kamfani ke da jiragen sama guda 251 don kai sakkoni a fadin duniya.