Likitoci Sun Ce A Kai Shugaban Zambia Kasar Waje

Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, sanye da bakar riga a zaune a wani wajen taro

Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, sanye da bakar riga a zaune a wani wajen taro

Shugaban Zambia Edgar Lungu, ya yanke jiki ya fadi a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ya ke gabatar da jawabi a lokacin bikin tunawa da ranar mata ta duniya.

Likitoci a kasar Zambia sun bayyana cewa sabon zabebben shugaban Kasar, Edgar Lungu, anda ya yanke jiki ya fadi a ranar Lahadi din da ta gabata, sun ce ya na bukatar ya je kasar wajen domin neman magani.

A jiya Mr. Lungu ya yanke jiki ya fadi a baina jama'a yayin da ya ke gabatar da wani jawabin ranar tunawa da mata ta duniya.

Ofishin shugaban kasar ya bayyana cewa ya na fama da wata cutar toshewar makogoro, wato cutar nan da ke tsuke makogoron bil adama, ta kuma haddasa ciwon kirji da zafi wajen hadiye abinci da ruwa.

A cikin sanarwar yau da aka fitar a yau Litinin, likitoci sun bayyana cewa ya na da matukar muhimmanci a yi amfani da na’u’rorin zamani wajen duba lafiyar Mr. Lungu, na’u’ro’ri irin wadanda babu su a Zambiya, saboda haka su ke ba da shawara a kai shugaban kasar waje domin samun lafiya.

Har ila yau likitocin sun ce an samu kwayoyin cutar zazzabin cizon sauro da gajiya tare da Mr. Lungu, mai shekaru 58.

Mataimakin shi Amos Chanda ya bayyana cewa gwaje-gwaje da aka yi wa shugaban daga baya sun nuna cewa Mr. Lungu na kuma fama da karancin sukari a cikin jinisa.

A dai watan Oktoban bara Mr. Lungu ya hau karagar mulki bayan da tsohon shugaban kasar Michael Sata ya rasu.

Mr. Sata shi ne shugaban kasar na biyu da ya mutu a kan karagar mulki cikin shekaru shida.