Shugaban kungiyar a jihar Inugu Dakta Celestine Chijioke Ugwoke ne ya yi wannan kiran a yayin da aka bude bikin makon likitoci wanda aka gudanar a Inugu, babban birnin jihar Inugu ranar Talata 25 ga watan Oktoba.
Ugwoke ya kuma ce ya kamata gwamnati ta dauki kwararan matakai don inganta albashin likitoci da kuma inganta yanayin aikinsu don su ci gaba da zama a kasar. Yana mai cewa likitocin ba suna barin kasar don son ransu ba ne, suna ficewa ne don su inganta rayuwarsu. Amma idan aka biya musu bukatunsu ko da rabin abin da suke so ne, ba likitan da zai fice daga kasar.
Likitan ya bukaci hukumomin kasar su bada fifiko a fannin kiwon lafiya kamar yadda za a ba bangaren tsaro da kuma tattalin arziki.
A yayin gudanar da makon likitocin na bana, Dakta Nnamdi Ezeugwuorie sakataren hulda da jama’a na kungiyar likitoci a jihar, ya ce likitoci zasu fi mayar da hankali ne wajen kula da lafiyar al’umma.
“Zamu je wurare dabam daban mu ga marasa lafiya kyauta kuma mu basu magani," a cewar Ezeugwuorie. Ya kara da cewa masu fama da rashin lafiya mai tsanani zamu basu magani sannan mu turasu asibitin koyarwa don a basu isasshen kulawa.’
Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe:
Your browser doesn’t support HTML5