Likitan Bogi Ya Kashe 'Yar Shekara Uku a Nasarawa

Kemis

Hukumar tsaro da ba da kariya ga al'uma wato Civil Defence, ta cafke wani likitan bogi bayan da ya halaka wata yarinya 'yar shekara uku a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya.

Yarinyar ta rasu ne bayan da ya yi kokarin kara mata jini, a lokacin da take fama da rashin lafiya.

Kwamandan rundunar Civil Defence a jihar, Muhammad Gidado Fari, ya ce Mudassir Muhammad wanda dalibi ne, ya bude shagon siyan magani da ake kira Chemist ba tare da yin rajista ba, inda ya ke bai wa jama'a magunguna idan ba su da lafiya.

Bayanai sun yi nuni da cewa, Mudassir bai tsaya a nan ba, har ya kai ga sakawa wannan yarinya jini inda ta kumbura har ta rasa ranta, duk da cewa ya san ba shi da kwarewar da zai yi irin wannan aiki.

Kwamandan ya ce za su kai shi kotu domin a tuhume shi da laifin kisa, duk da cewa matashin ya amsa laifinsa, kuma ya yi kira ga al'umma jihar da su yafe masa.

Shugaban kungiyar likitoci a jihar Nasarawa, Dakta Bulus Peter, ya shawarci jama'a da su guji zuwa wuraren ba da magani da ba a tantance ba.

A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga jihar Nasarawa:

Your browser doesn’t support HTML5

Likitan Bogi Ya Kashe 'Yar Shekara Uku a Nasarawa