An gano wani kabari makare da gawarwakin mutane 36 a kusa da birnin Benghazi a kasar Libiya.
Da alamar kashe mutanen aka yi a lokaci guda, to amma ba a san ko su waye mamatan ba. Wani rahoto na cewa wasu daga cikin gawarwakin na saye da tufafin ‘coat’ a yayin da wasu kuma ke sanye da kayan wasan guje-guje.
Ghassan Salame, Shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya, MDD a Libiya, ya fadi a wata takarda bayani cewa “wannan aika-aikar ta bakanta ma ni rai” ya na mai kiran da a yi binciken al’amura irin wannan.
Duka gwamnatocin Libiya biyu kishiyoyin juna: da wadda duniya ta amince da ita da kuma wadda ke karkashin jagorancin Khalifa Haftar, duk sun yi tir da kashe mutanen, sun kuma yi kiran da a yi bincike.
Libiya ta kasance cikin rudami da dambarwar siyasa tun bayan kashe dadadden shugabanta mai mulkin kama karya Moammar Gadhafi a 2011.