Libiyawa Sun Afka Cibiyar Gwamnatin Wucin Gadi a Benghazi

Masu zanga-zanga a Benghazi

Masu zanga-zanga sun kutsa kai sun shiga cibiyar mulkin rikon kasar Libiya sun gabatar da koken su

A jiya Asabar tulin masu zanga-zanga a kasar Libiya sun yi amfani da gurnetin da ake jefawa da hannu sun kutsa da karfi cikin helkwatar Majalisar mulkin wucin gadin kasar a birnin Benghazia gabashin kasar , domin su nuna bacin ran su da tafiyar hawainiyar da ake yi wajen aiwatar da sauye-sauye a kasar.

Shaidu sun ce jama’ar Benghazi, mahaifar marigayi tsohon shugaban kasar Moammar Ghadafi, na neman lallai sai sabbin shugabannin kasar sun kara yin abubuwa a bayyane ba rufa-rufa. A cikin masu zanga-zangar har da tsoffin ‘yan tawayen da suka ji ciwo a yakin da su ka fafata da sojojin Gadhafi.

Wannan al’amari ya faru ne ana sauran kwana daya a sanar da sabon daftarin dokar zaben kasar.

A farkon wannan wata gwamnatin kasar Libiya ta wallafa daftarin wanda ya haramta tsayawa takarar neman wani mukami ga wadanda su ka yi aiki a karkashin mulkin marigayi Gadhafi ko kuma su ka samu wata fa’idar kudi a zamanin mulkin shi.

Daftarin ya haramta shiga takara ga tsoffin jami’an da ake zargi da ganawa ‘yan kasar Libiya ukuba ko wadanda suka saci dukiyar kasa ko ‘yan rundunar askarawan juyin juya hali, da kuma mayakan adawa da suka yi sulhu da marigayi Gadhafi.

Haka kuma daftarin ya tanadarwa mata kujeru 20 a cikin majalisar dokokin kasar mai wakilai 200. An tsaida cewa za a yi zabe a cikin watan yuni mai zuwa.

Amma shugaban Majalisar mulkin wucin gadin kasar Mustafa Abdel Jalil ya kara jaddada cewa dokar daftari ne har yanzu , kuma za a iya yi ma ta gyara.