Leicester: Zamu Yi Duk Abun Da Ya Kamata Kada Rodgers Ya Tafi

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City tana yunkurin sabunta kwantirakin mai horas da 'yan wasanta Brendan Rodgers.

Kungiyar ta ce zata sake sabuwar yarjejeniya tsawaita kwantirakin ne, sabo da ta haramta masa zuwa kulob din Arsenal, da ake alakanta shi da zuwa bayan ta sallami kocinta a watan da ya gabata.

Kocin mai shekaru 46 da haihuwa, ya fara aiki da Leicester City a cikin watan Fabrairun bana, bisa yarjejeniyar shekaru uku da rabi, akan albashi fam miliyan biyar a shekara.

Inda yanzu haka kungiyar take mataki na biyu daga saman teburin Firimiya lig na kasar Ingila, wanda ko aranar Larabar da ta wuce ta lallasa kungiyar Watford da ci 2-0.

Kungiyar ta ce kuma tayi hakanne domin irin yadda ya dawo da martabar kungiyar a idon duniya, wadda yanzu haka tattauna tayi nisa tsakaninta da kocin kan sabon kwantirakin nasa.

A ranar Lahadin nan mai zuwa Leicester zata ziyarci kulob din Aston Villa, a wasan mako na 19 cikin gasar firimiyar bana.