Leicester City Zata Sake Yunkurin Sayen Ahmed Musa

Nigeria's Ahmed Musa celebrates after scoring his team's second goal against Argentina during their 2014 World Cup Group F soccer match at the Beira Rio stadium in Porto Alegre June 25, 2014.

Kungiyar Leicester City dake saman teburin wasannin Firimiya Lig a Ingila, tana adana kudi har Fam miliyan 23 domin ta sake kokarin sayen dan wasan Najeriya Ahmed Musa, a lokacin daminar bana.

Jaridar Mirror ta ce a watan da ya shige na Janairu, shugaban kungiyar Leicester City, Claudio Ranieri, yayi bakin kokarinsa domin janyo kyaftin din na ‘yan wasan Super Eagles zuwa filin wasa na King Power, amma sai kungiyar da Musa yake buga ma kwallo yanzu, CSKA Moscow, ta ki yarda.

Kungiyar CSKA ita ce a kololuwar teburin Firimiya Lig na Rasha, kuma zata fuskanci Dynamo Kiev a zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai. Kungiyar ta yi imanin cewa kyale Ahmed Musaa ya koma wata kulob zai raunana yunkurinta na lashe wadannan kambuna a sauran kakar kwallon bana.

Kungiyar CSKA Moscow tana kokarin rike Musa, wanda ya sanya hannu kan sabon kwantarakin shekaru 4 a shekarar da ta shige, na tsawon kwantarakinsa, har ma da kari.

Amma da alamun yana shirin taba leda a gasar Firimiya ta Ingila, kuma an ba shi tabbacin cewa Ranieri yana sha’awar yadda yake murza tamaula, don haka zai ci gaba da kokarin saye shi zuwa Leicester City.

A watan da ya shige, Leicester ta taya Musa a kan Fam miliyan 15, daga baya ta kara zuwa famn miliyan 18 da dubu 700, amma duk CSKA ta sa kafa ta shure.

A bayan Leicester, akwai wasu kungiyoyin na Firimiya Lig na Ingila dake sha’awar sayen Musa, cikinsu har da Stoke City, Southampton da kuma Manchester United.