Legas Ta Musanta Jita-jitar Tserewar Dan Italiya

Wasu ma'aikatan lafiya suna feshi domin kashe kwayar cutar coronavirus a Tehran babban birnin Iran, ranar 26 ga watan Fabrairu, 2020.

Hukumomi a jihar Legas da ke kudancin Najeriya, sun musanta rahotannin da ake yadawa ta kafofin sada zumunta cewar, dan kasar Italiyan nan mai dauke da cutar coronavirus ya tsare daga asibitin da ake kula wa da shi.

Hakan na faruwa ne yayin da gwamnati ta ce an fara gano wasu daga cikin fasinjojin da suka shiga jirgin Turkiya tare da dan kasar ta Italiya.

Mutumin dan Italiya, wanda ba a bayyana sunansa ba, na aiki ne da kamfanin siminti na Lafarge Africa Plc a jihar Ogun da ke makwabtaka da Legas.

Gwamnan jihar Ogun, yayin wani taron manema labarai na daban, ya ce, an kebe mutane 28 da ke aiki a kamfanin siminti.

Ministan lafiya, Osagie Ehanire a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya, Abuja, a nashi bangaren ya ce hukumomin Najeriya na daukan matakan da suka dace don hana yaduwar cutar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Legas Ta Musanta Jita-jitar Tserewar Dan Italiya