Dokar hana zirga zirgan wadannan ababan hawa za ta fara aiki ne daga karfe tara na dare zuwa shida safe.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin sufurin jahar mai dauke da sa hanun Sakataren ta, ta nuna cewa, wannan doka ba sabuwa ba ce, za dai kawai a farfado da ita ne ganin yadda ake fuskantar karin asarar rayuka a jahar.
Saboda haka dokar ta umurci ‘yan sanda da sauran malaman hanya da su tabbatar masu manyan ababan hawa sun bi umurnin dokar.
Tuni dai mazauna garin suka fara tofa albarkacin bakinsu game da wannan doka inda wasu sua yi na’am da ita yayin da a bangaren wasu aka sami akasin hakan.
“Dokar ta yi daidai, sai da kyan shi a maida da ita zuwa karfe goma na safiya zuwa tara na dare, ni a gani na, ba manyan motoci ne ladai ke haddasa hadari ba, kamata ya yi a duba matsalar kananan hanyoyi da kuma cunkoso.” In ji Mr Ojo.
A karshen makon da ya gabata ne, aka yi asarar rayukan mutane kusan 15, a wasu hadurra a birnin na Legas da kuma hanyar zuwa Ibadan, inda wata mota dauke da kwatenar siminti da fada kan wata mota karama ta kuma kashe fasinjoji hudu da ke cikin motar.
Ga karin bayani a wannan rahoton na wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibril daga Legas.
Your browser doesn’t support HTML5