Kungiyar mata lauyoyi reshen jahar Pilato ta ce za ta jajirce don ganin an kawo karshen cin zarafin mata da yara a Najeriya.
WASHINGTON, D.C. —
A wani taron kara wa juna sani na mako guda da kungiyar mata lauyoyin suka shirya a Jos, shugaban kungiyar Mary Izam ta ce yawan rahotannin cin zarafi da suka samu lokacin dokar hana yawo saboda cutar Coronavirus a Jahar Pilato ya sa su damarar yaki da mugayen dabi’un.
Malam Nurudden Usaini Magaji, wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron bitar, ya ce dole sai dukkan masu ruwa da tsaki sun hada hannu don shawo kan wannan lamarin.
Tsohuwar kwamishinan ma’aikatar mata da walwalar jama’a a jahar Pilato, Barista Olivia Dazyem, cewa ta yi kamata yayi a yi garambawul wa dokokin da suka shafi cin zarafin mata da yara.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5