Lauyan ‘yan Boko Haram da ake tuhuma ya zargi babbar kotun tarayya da nuna son rai bias ga yadda ake tsare da ‘yan Boko Haram din a Hukumar DSS maimakon a gidan kaso.
Lauyan na shakkar ‘yan Boko Haram din ko zasu samu hukunci mai adalci.
Saidai a zantawa da yayi da manema labarai, lauyoyin gwamnati na cewa sun shirya tsaf su cigaba da shari’ar.
A wani yunkuri na daban, mai shari’a John Tsoho ya yanke hukuncin cigaba da yin shari’ar. Yanzu za’a mayar da batun babban kotun tarayya domin a mikawa wani alkalin shari’ar.
Barrister Ibrahim Tukur El-Sudi, lauyan tsarin mulki, yace ‘yan Boko Haram basu yarda da kotun kasar ba saboda haka zasu cigaba da yin korafe korafe har a gaji a yi watsi da korafin nasu.
Wani lauyan ma cewa yayi ‘yan Boko Haram din sun wuce gona da iri saboda wasu dalilai da ya lissafa.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5