Lashe Gasar Duniya Ke Gabana Yanzu

Zakaran kwallon tebur na bana a gasar kwallon tebur na Asoju Oba, na Najeriya, Rilwan Akanbi, ya ce abinda yake hari nan gaba shine lashe kofin duniya na matasa na kwallon tebur wanda za’a gudanar a kasar Afirka ta kudu.

Ranar laraban nan mai zuwa ne za’a fara gudanar da gasar na duniya a Cape Town ta Afirka ta kudu.

Akanbi, wanda ya lashe gasar bana na Najeriya, a filin wasa na Teslim Balogun, dake Legas, zai wakilici Najeriya, a gasar na duniya watau “International Table Tennis Federation World Junior Championships” da wasu ‘yan wasa kamar Azeez Solanke, Amadi Omeh, Tobi Falana, Esther Oribamise, Ajoke Ojomu, Halima Ayinla da Agnes Onoja.

Rilwan Akanbi, ya ce yayi murna matuka da wannan nasara da ya samu, kuma abinda yake gabashi a yanzu shine lashe labar yabo na gasar tebur na kasa da kasa wanda za’a gudanar a Afirka ta kudu.