Larabawa Na Fatan Hillary Clinton Ta Lashe Zaben Shugaban Amurka

Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat

Binciken da aka yi akan ra'ayin larabawa dangane da zaben Amurka mafi yawa suna fatan Hillary Clinton ce ta jam'iyyar Democrat zata lashe zaben domin a ganinsu zata fi taimaka masu fiye da abokin hamayyarta.

Larabawa a kasashe daban-daban da suka kama daga Iraqi zuwa Tunisia suna bibiyar zaben shugaban kasa a nan Amurka kuma akasarin larabawan duk suna son ganin yar takatar Democrat Hillary Clinton ta lashe zaben, saboda suna kyautata zaton itace kawai zata anfani kasashen nasu, a cewar wani bincike.

Wannan binciken da Cibiyar Nazarin Harakokin Kasashen Larabawa ta nan Washington DC ta gudanar a kasashe takwas, ya gano kashi 66 cikin 100 sun fi ra’ayin Clinton ta dare kan shugabancin Amurka, a yayind da kashi 11 cikin dari kadai ne ke ra’ayin dan takarar Republican Donald Trump.

Binciken ya jiyo ra’ayoyin mutane 3,200 a kasashen Algeria, Egypt, Kuwait, Morocco, yankunan Falasdinu, Saudi Arabia da kuma Tunsia daga ran 21 zuwa 31 ga watan Oktoba. Duka-duka an jiyo ra;ayoyin mutane dari hur-hudu ne a kowace kasa daga cikin kasashen da aka gudanarda binciken a cikinsu.