Laraban nan idan Allah ya yarda shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria zai kai ziyara kasar Kamaru. Shugaba Buhari da takwaran aikinsa na kasar Kamaru Paul Biya zasu tattauna akan yaki da yan Boko Haram
Da misalin karfe goma na safe agogon kasar Kamaru, aka shirya shugaba Paul Biya zai tarbi shugaba Buhari a filin saukar jirage saman birnin Yaounde.
Bayan shugabanin biyu sun gama yin shawarwari, an shirya shugaba Buhari zai gana da 'yan Nigeria mazauna kasar Kamaru.
Ranar Alhamis aka shirya shugabanin biyu zasu gabatar da sanarwar hadin gwiwa akan batutuwan da suka yi shawarwari akan su.
Shugaba Buhari zai kai ziyara kasar Kamaru makamancin wadanda ya kai jamhuriyar Niger da kuma kasar Chadi bayan ya dare kan mulki, a wani yunkurin ganin yadda kasashen makwaptan juna zasu yaki yan Boko Haram, wadanda suke ci gaba da kai hare hare da karkashe mutane a kasashen guda hudu.
Your browser doesn’t support HTML5