Gwamnatin Najeriya, da mahukuntan kasar sun bada umurnin cewar tun daga farkon wannan shekarar ta 2019, dole ne kowane dan kasa ya samu lambar shaidar zama 'yan kasa, idan suna so su more wasu abubuwa wadanda ake samu daga ma'aikatu da hukumomin gwamnati.
Wannan umurni bai yi wa wasu 'yan kasa dadi ba, Shugaban Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Arewa Maso Gabas, Saleh Bakoro Sabon Fegi Damaturu, wanda ya ce hukumar ba ta yi dai-dai ba, yana ganin tsoro ta ke ji kar a sa ido akan ayyukan ta, shi ne ya sa ta fito da wannan batu na samun lambar zama dan kasa.
Yana mai cewa a baya ma hukumar ta ce a yi katin zama dan kasa wanda har yanzu shekaru 12 kenan ba a kamalla aikin ba, ganin cewa cibiyoyin rajista 1,000 ne kawai hukumar ta bude wa 'yan kasa sama miliyan 185.
A jawabinsa, Shugaban Hukumar bada katin zama dan kasa Injiniya Aliyu Aziz Abubakar, ya ce Najeriya ce kasa ta 7 mai yawan mutane a duniya, kuma ita ce ba tada tsarin wannan lambar ta zama dan kasa, ya ce idan ana so a yi tsare-tsare da al'umma za su samu romon mulkin da ake yi, lallai dole ne a samu wannan lambar da kuma katin zama dan kasa.
Yawancin abubuwa da ke bukatan wannan lambar sun hada da harkar kiwon lafiya, makaranta da kuma mallakan filaye.
Hajiya Aisha Shuaibu Galma, ta ce hanzari me ake yi, yanzu lokaci ne na zabe, a bari mutane su fuskanci abu daya a lokaci daya, saboda haka tana ganin cewar akwai bukatar idan an ciza sai hura.
Wannan tsari na lamba da kuma katin zama dan kasa zai baiwa Gwamnati damar sanin su waye 'yan kasa, kuma suwaye bakin haure, zai kuma bada damar sanin mutane mawa ke morewa shirye shirye da tsare tsare da gwamnatin ke yi domin talakawanta.
Ga rahoton Madina Dauda daga Birnin Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5