Yau dadalinvoa ya sami bakuncin fitattcen jarumin Kannywood wanda ya ga jiya yaga yau a harkar fina finan Hausa Rabiu Rikadawa, wanda ya fara sana’ar fin a sakamakon sha’awa da ya samu tun yana makarantar sakandire a ire-iren kungiyoyin makaranta wato Clubs.
Jarumin ya bayyana cewa mafi yawancin lokuta idan aka kusa ba su hutun makaranta, su kan gudanar da wasannin clubs, yayinda watarana ya fito a matsayin ‘Inyamiri’ daga nan ne ya fuskanci cewar ya kamata ya mai da wasan kwaikwayo a matsayin sana’a.
Rikadawa ya kara da cewa ya fara wasan kwaikwayo tun a shekarar 1986, bayan mutane sun fara bashi shawarar ya kamata ya kai fasaharsa gidajen rediyo da talabijin har lokacin da ta girma ya tsunduma cikin masana’antar kannywood.
Rabi’u Rikadawa dai ya fito a fina finai da dama kamar su fim din Dila, Shiga Sharo Ba Shanu da sauransu, bayan ya mai da wasan kwaikwayo a matsayin sana’a.
Ya ce harkar fim a da, da yanzu lallai akwai bambancin, domin a da ba’a rubutu labari, abinda ake yi kawai shine fadawa jarumi abinda ake so ya aikiata, wanda a yanzu harta kayan ayyukan sun bambanta da na da.
Kuma a yanzu ana ciniki kafin mutum ya fara fitowa a fina-finai da sauransu sabanin yadda ake yi a da.
Your browser doesn’t support HTML5