Lagos: Hukumar Kwastam Ta Kama Kayayyaki Na Sama Da Naira Biliyan Biyu

Shugaban Hukumar Kwastam

A wani taron manema labarai da hukumar ta kwastan ta gudanar ta ce muggan kwayoyin tramadol da codeine da aka haranmta shigowa da su ba tare da takardar hukumar NAFDAC ba, sun kai na fiye da naira miliyan 250.

Dr Mohammmed Ali shine kwanturola mai kula da wannan shiya ta daya dake Legas kuma ya yi Karin haske akan kame kame da hukumar ta kwastan din keyi, ya ce yanzu haka akwai kaji da sauran abubuwan da aka kama, irinsu kwayoyi da aka haramta shigowa dasu da Mai da iniyan hemp ko wiwi duk an kama kuma ana ci gaba a kama duk wasu kayan da aka haramta shigowa asu cikin gida.

Sha ko sayar da muggan kwayoyi dai abu ne daya zama ruwan dare a tsakanin matasa, don haka wakilin Muryar Amurka ya tambayi wasu mazaunan legas yarda sukaji da wannan kamu na muggan kwayoyin da akayi, a cewar wani matashi yaji dadin wannan mataki da kwastan ta dauka na kama muggan kwayoyi a kasa, hakan zai taimaka wajen rage muggan kwayoyi a kasa,don haka wannan abin yabawa ne matuka.

Sauran kayayyakin da kwastan din ta kama dai sun hada da motoci na alfarma da kayan gwanjo.

Saurari rahotan Babangida Jibrin daga Legas.

Your browser doesn’t support HTML5

A Najeriya, Costoms Ta Kama Kayan Sumogal Na Fiya Da Naira Biliyan Biyu A Legas