Lagos: An Kubutar Da Mata 19 Daga Masana'antar Sarrafa Jarirai

‘Yan sanda a Legas sun ba da sanarwar kubutar da wasu‘ yan mata 19 masu juna biyu daga ‘masana’antar jarirai’ a yankin Ayanwale da ke Ikotun.

An yi kamun ne a ranar 19 ga Satumba.

A wata sanarwa, mai magana da yawun 'yan sandan Jihar Legas, Bala Elkana ya ce matan shekarunsu ya kama daga 15 zuwa 28.

An kama biyu daga cikin wadanda ake zarginsu da hannu da wannan badakala.

A cewar Mista Elkana, dake zaman jami'in bincike a ofishin' yan sanda na Isheri-Osun karkashin jagorancin Sufeto Janar Chike Ibe, sun yi aiki ne a kan bayanan sirri daga wata majiya mai tushe wacce ta kai ga kama wadanda ake zargin.

"Wadanda suka samu juna biyu sun fito daga jihohin Ribas da Cross River da Akwa Ibom da Anambra da Abia da kuma Imo."

An sato matan ne da niyar a a yi masu fyade, in sun samu juna biyu sun haihu, a sayar da jariran ga masu saye. Tun farko ana yaudarar yan matan da cewa za a basu aikin yi a Legas kafun kawo su.

Mutane biyu da ake zarginsu, sun hada da Happiness Ukwuoma mai shekaru 40 da haihuwa, da Sherifat Ipeya ‘yar shekara 54 da haihuwa.. Wadanda ake zargi suna aiki ne a gidan saida jariran a matsayin ma’aikatan jinya, duk da cewa basu da wata kwarewa a fannin aikin jinya.

Har ya zuwa yanzu dai ba a kama babbar wadda ake zargi da ita ce shugabar wannan masana'anta da ake kira Madam Oluchi, kuma 'yan sanda suna kan kokarin nemanta.

Ana sayar da jariran ne tsakanin N300,000 zuwa N500,000 ya danganta da jinsinsu. Ana sayar da yara maza akan N500,000 da 'yan mata akan N300,000. ”