LAFIYARMU: Yadda Yanayin Wasu Wuraren Aiki Ke Shafan Lafiyar Kwakwalwa

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce matsananciyar damuwa mai alaka da aikin da mutun ke yi, ta na samuwa ne sakamakon irin yanayin aikin da mutun ke yi, ko kuma yanayin da ya ke yin aikin, ko jadawalin aikin na shi ko kuma rashin samun damar karin girma ko cigaba a wurin aiki.