Kasar Ingila ta bayyana sunan dan wasan gaba na kungiyar kwallon Kafa ta Tottenham, Harry Kane, a matsayin Kaftin din kungiyar kwallon Kafa ta Ingila.
Dan wasan zai jagoranci ‘yan wasan Ingila a gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Rasha, a bana 2018.
Harry Kane, me shekaru 24 da haihuwa ya zurara kwallaye 41 a dukkan wasannin da ya buga na shekarar da ta gabata inda kungiyar Tottenham ta kammala a mataki na uku a gasar Firimiya lig 2017/18 ta kasar Ingila.
Ya kuma taimaka wa kasarsa ta Ingila wajan samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za'ayi musamman a wasansu da kasar Scotland, wanda suka tashi 2-2 dan wasan shi ya jefa kwallo da aka tashi hakan a mintocin karshe wanda haka ya bata damar hayewa.
Kane, ya zurara kwallaye 12 a wasanni 23 da ya buga wa kasarsa ta Ingila.
Kocin kasar Ingila Southgate, ya ce dama a cikin ‘yan wasa biyu ne yake so ya zabi daya daga ciki ya zamo Kaftin a kungiyar da Henderson, na Liverpool. da kuma Harry Kane. Amman daga bisani ya yanke shawarar bai wa Harry Kane.
Kasar Ingila dai zata fafata da Najeriya a wasan sada zumunci ranar 2 ga watan yuni 2018, a shirye shiryensu na zuwa gasar cin kofin duniya inda zasu fara bugawa wasansu na rukuni tsakaninsu da Kasar Tunisiya ranar 18 ga watan Yuni.
Your browser doesn’t support HTML5