Dan kwallon gaban na kungiyar Paris Saint Germain mai suna Kylian Mbappe ya ci kyautar Golden Boy ta wannan shekarar wanda ke nufin cewa dan wasan ya yiwa duk wani dan kasa da shekaru ashiri a Turai fintinkau a faggen taka leda.
‘Yan jarida ne sukai zaben wanda ya chanchanta a fadin duniya inda wata jarida a kasar Italiya wato Tittosport ta bayyana wanda yayi nasara a yau litinin.
Mbappe wanda ya ci kwallo hudu sannan ya taimaka sau 11, a kungiyar ya samu daukaka a duniya ta kungiyar Monaco a kakar wasannin da ta gabata.
An bada aron dan wasan mai shekara goma sha takwas zuwa kuniyar Prc des Princes dan wasan wanda a baya yaci kyaututtukja takwas a kasar Faransa zai zama dan kungiyar na dindindin a kakar wasanni mai zuwa akan zunzurutun kudi Euro miliyan dari da tamanin.
Mbappe ya ci kyautar ne inda ya doke Gabriel Jesus, na Manchester City da Ousmane Dembele na Bercelona da Gianluigi Donnarumma na Milan.
Dan wasan ya shiga jerin wandanda sukaci kyautar a da wanda ya kunshi Lionel Messi, Paul Pogba da Isco.