Kammar yadda masu iya Magana suka ce duk rai na kaunar mai kyautata masa, haka lamarin yake musamman bangaren masoya, domin kuwa kamar yadda muka saba kawo maku shirin samartaka na dandalinvoa a kowane karshen mako inda muke jin ra’ayoyin samari da ‘yan mata akan batutuwa makamantan wadannan.
A wannan karon shirin samartaka ya sami zantawa da matasanne akan tasirin kyauta, wato irin rawar da kyauta ke takawa wajan kara dankon soyayya da zumunci a tsakanin abokai, masoya a kuma sauran jama’a baki daya.
Komai wadatar da Allah ya yi wa bawansa, kyauta kan faranta masa zuciya komai kankantarta haka-zalika shima idan yana yawaita bada kyauta komai kankancinta, jama’a kan kara kusantarsa, da kuma kwatanta shi a matsayin mai kirki.
Abin tambaya anan shine, idan kyauta nada matukar alfamu a tsakanin jama’a baki daya, shin ko akwai wani bangare da kyauta keda illa?
Ana iya aiko mana da amsar wannan tambaya kokuma ra’yoyinku ta muryoyi dangane da tasirin kyauta, da kuma illarta idan akwai ta shafinmmu na facebook, kokuma ta shafinmu na kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +1 202-577-5834
Your browser doesn’t support HTML5