Kyari: Shugabannin Nijar, Ghana Sun Yi Wa Buhari Ta'aziyya

Shugaban Nijar, Issouhou Mahamadou

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadou Issouhou da takwaran aikinsa na Ghana, Nana Akuffo-Ado, sun mika sakon ta’aziyyarsu ga Shugaba Muhammadu Buharim, bisa rasuwar Abba Kyari.

Kyari, wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayyar Najeriya ya rasu yana mai shekara 67 a ranar Juma’a bayan ya yi fama da cutar coronavirus.

“Shugaba Nana Akuffo-Ado na kasar Ghana da Shugaba Muhammadou Issouhou na Jamhuriyar Nijar sun kira shugaba Buhari.” Kakakin Buhari Garba Shehu ya fada a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Baya ga haka, tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Benin, Yayi Boni shi ma ya kira shugaba Buhari domin mika ta’aziyyarsa.

A cikin gida kuwa, tsoffin shugabannin Najeriya, Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo, Gen. Yakubu Gowon da Abdulsalam Abubakar, su ma duk sun kira Buhari domin yi masa ta’aziyya.