Muryar Amurka tayi tattaki zuwa Majalisar Dattawan Najeriya inda ta zanta da Sanata Barau Jibrin wanda a gidansa dake Kano aka samu motocin da aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan dari biyu da casa'in da takwas.
Da Muryar Amurka ta zanta dashi ga abun da yake cewa " To ai babban abu shi ne ita dimukradiya ba wanda zai ce ya fi kowa wato sanin abun da ya dace a yi. Idan ka zo da abunka aka fada ma kan cewar wannan abun a gyara ai ba wata matsala ba ce, sai a duba a zauna..Duk wadannan abubuwa bai ma dace a zo ana magana akan wadannana abubuwa ba yanzu. Abun da ya dace shi ne muna cikin wani yanayi kamata mu hada kanmu ga baki daya muga zamu taimakawa wannan kasar. Amma a zo a zauna a dinga maganganu wadanda babu tushe, misali a bar abun da yake damun kasarmu mu je muna ta wani abu na daban. Ina ganin wannan ba daidai ba ne".
Ga rahoton Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5