Hukumar kwastam tare da hadin gwiwar hukumar kayyade Ingancin magunguna da abinci ta Najeriya NAFDAC sun kona tarin katan-katan na kwayoyin Tramadol da aka kiyasta kudinsu, zasu kai kimanin naira biliyan N14.7.
An kona akwatina 58 da ke kunshe da tarin kwayoyin tramadol da aka shigo da su cikin gida Najeriya takan iyakokin kasar, wanda hukumar ta kwastan ta kama.
Hakan na cikin kudin gwamnatin Najeriya na kokarin hana anfani da kwayoyin ba bisa ka’ida ba, a lokacin kona wadannan kwayoyi, shugaban kwamitin kuma wakilin kwanturolan kwastam a wajen Aminu Dahiru, yace wannan aiki a yankin kudan cin Najeriya, shine na farko kafin su rankaya zuwa sauran jihohin Najeriya, irin su Fatakwal, Kaduna da Bauchi.
Yayi karin haske akan lafiyar da kasa zata samu ta hanyar kona irin wadannan kayayyakin da ake shigo da su ba da iziniba. Matakin zai taimak wajen hana matasa shan kwayoyi da kuma kawo karshen aikace-aikacen ta’addanci a kasa.
Domin kuwa akasarin masu aikata muggan laifuka na anfini da magungunan, kama dagam asu garkuwa da mutane zuwa masu fashi da makami ko aikata kisan gilla.
Ga rahoto na musamman daga Legas, wanda Babangida Jibrin ya hada.
Your browser doesn’t support HTML5