Kwararrun Hukumar WHO Sun Isa China Don Fara Bicike Kan COVID-19

Kwayar cutar coronavirus

Kwayar cutar coronavirus

Wata tawagar kwararru daga WHO hukumar lafiya ta duniya ta isa China don shirin fara bincike akan asalin annobar coronavirus.

Cutar da ke haddasa COVID-19, wadda aka yi imanin daga dabbobi ta fara kafin ta fara shafar bil’adama, a wata kasuwar sarin kayayyaki da tuni aka rufe ta a birnin Wuhan da ke tsakiyar China ta fara bulla a cikin shekarar da ta gabata.

An Rufe Kasuwar Wuhan

An Rufe Kasuwar Wuhan

Wasu masana daga hukumar WHO da ke Geneva, da suka kware a fannin lafiyar dabbobi da nazarin yaduwar cututtuka a cikin al’umma, zasu gana da takwarorin aikinsu na China a Beijing ranar 11 ga watan Yuli don fidda sharudda da kuma abubuwan da zasu yi bincike akansu, a cewar Tarik Jasarevic, wani mai Magana da yawun hukumar WHO.

“Makasudin nazarin shine zurfafa bincike akan fahimtar dabbobin da cutar COVID-19 ta fara kamawa da kuma yadda dabbobin suka sanya wa mutane cutar, a cewar Jasarevic a wata hira da Muryar Amurka.